Claudio Ranieri na muradin komawa Ingila

ranieri Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Claudio Ranieri

Tsohon kocin Roma Claudio Ranieri ya ce yanason ya kara komawa horadda 'yan kwallo a gasar premier ta Ingila

Dan shekaru hamsin da tara wanda a baya ya jagoranci Chelsea daga shekara ta 2000 zuwa 2004 ya ce zai yi murnar sake komawa Ingila.

Yace"Ina son gasar kwallon Ingila, zan so in kara komawa gasar premier".

A baya anyi hasashen kocin Chelsea Carlo Ancelotti zai shafe lokaci mai tsawo a matsayin koci a Stamford Bridge,amma dai Ranieri yace nasara ce kadai ke baiwa kocin damar dadewa a mukami.

Ranieri ya kara da cewar :"Manajoji na fusknatar matsin lamba, ko su samu nasara ko kuma a koresu".

Mai kulob din Chelsea Roman Abramovich ne ya kori Ranieri a shekara ta 2004 inda attajirin na Rasha ya maye gurbinshi da Jose Mourinho amma har yanzu ba a cimma burin lashe gasar zakarun Turai ba.