'Yan sanda sun kwace motar Alex Song na Kamaru

song Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alex Song

'Yan sanda a Ingila sun kwace motar dan kwallon Kamaru wanda ke taka leda a Arsenal Alex Song saboda gudu akan hanyar Hertfordshire.

A ranar Alhamis ne 'yan sanda suka kama dan kwallon mai shekaru ashirin da uku yana sharara gudu akan titi amma sai yaki tsayawa ya bada bayanai.

Daga bisani sai 'yan sandan suka lallabeshi suka kwace motar kuma suka bukaceshi ya kawo takardar izinin tuki dana inshora. Ana zargin yana gudu akan tazarar kilomita hamsin kowace sa'a, akan titin da ba a wuce kilomata talatin kowace sa'a.

Kakakin 'yan sanda ta ce dan kwallon ya kasa bada takardun da 'yan sanda suka bukaci ya basu.

An baiwa Song kwanaki bakwai ya bada takardun da aka bukata daga wajenshi kafin a dauki mataki na gaba akanshi.