2014:A mako mai zuwa Afrika zata san gurabenta

fifa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shalkwatar Fifa a Switzerland

A mako mai zuwa Afrika zata san yawan kasashen da zasu wakilceta a gasar cin kofin duniya da Brazil za ta dauki bakunci a shekara ta 2014.

Hukumar kwallon kafa ta duniya-Fifa za ta tattauna inda kowacce nahiya zata san yawan gurbin data samu daga cikin gurabe 31 a yayinda Brazil keda tabbas a matsayinta na mai masaukin baki.

Kasashe shida ne suka wakilci Afrika a shekara ta 2010, amma bisa dukkan alamu ba zata samu yawan haka ba a shekara 2014.

A ranakun biyu zuwa uku na watan Maris ne kwamitin gudanarwar Fifa zata tattauna a Zurich.

Har wa yau Fifa zata yanke hukunci akan kasar da za a baiwa damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata a shekara ta 2015 inda Zimbabwe da Canada ke nema.

Ghana zata sani ko zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniya na 'yan kasada shekaru 17 a shekara ta 2003.