Arsenal ta sayi dan kwallon Barcelona Jon Toral

wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsene Wenger

Arsenal ta sayi wani matashin dan kwallon Barcelona Jon Toral wanda ke bugawa karamar kungiyarta wato Youth Academy.

Barcelona ta tabbatar da cewar dan kwallon mai shekaru goma sha shida Jon Toral zai bi sawun Cesc Fabregas zuwa Gunners a kakar wasa mai zuwa.

Rahotanni sun nuna cewar Arsenal ta biya pan dubu dari uku da hamsin akan Toral wanda ke buga wasa a tsakiya.

Toral ya taho kamar yadda Fabregas da Fran Merida suka kulla yarjejeniya da Arsenal suna matasa.

Arsenal har wa yau ta sayi Ignasi Miquel mai shekaru goma sha takwas daga Barcelona a shekara ta 2008.