Ban ji dadin canjaras din da muka buga ba- Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce bai ji dadin canjaras din da kungiyar ta buga da Marseille ba a gasar zakarun Turai.

Idan dai aka samu ci kuma aka tashi kunnen doki a bugu na biyu da za a yi a Old Trafford a ranar 15 ga watan Maris, an fidda United kenan daga gasar.

"Zura kwallo a tattaki na da mattukar mahimmanci, ba mu samu mun zura kwallo ba, kuma ban ji dadin hakan ba," In ji Ferguson.

Ferguson ya ce wasan bai kayatar ba ganin cewa babu kungiyar da ta zura kwallo.