Walcott ba zai buga gasar cin kofin Carling ba

Dan wasan Arsenal Theo Walcott ba zai samu buga wasan karshe da kungiyar za ta kara da Birmingham a gasar cin kofin Carling a ranar lahadi saboda raunin.

Walcott ya turgude idon sahunsa ne a gasar Premier a wasan da Arsenal ta doke Stoke City da ci daya mai ban haushi.

"Ya samu rauni a idon sahun sa domin haka ba zai samu buga wasan na gaba ba," In ji Arsene Wenger.

Wenger ya ce za'a kara gwada lafiyar kyaftin din kungiyar Cesc Fabregas domin ganin tsananin raunin da ya samu a wasan shima.