Fabregas ya samu rauni

Kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas ba zai samu bugu wasan karshe ba a gasar cin kofin Carling a ranar lahadi, saboda yana fama da rauni a cinyarsa.

Dan wasan ya samu raunin ne a wasan da kungiyar ta buga da Stoke City a ranar laraba inda ta doke kungiyar da ci daya da nema.

A yanzu haka dai dan wasan ba zai buga da takwaransa Theo Walcott wanda shima ya samu rauni a wasan.

"Raunin bai yi tsanani ba, amma ba sai samu buga wasa ba a ranar lahadi." In ji Wenger

"Ba san tsawon lokacin da zai yi jinya ba."

Akwai yiwuwar Robin van Persie da Laurent Koscielny da kuma Abou Diaby za su samu buga wasan.