Ba zamu sayarda Fabregas ba-Gazidis

fabragas
Image caption Cesc Fabregas

Shugaban Arsenal Ivan Gazidis ya ce kulob din baida muradin sayarda kaptin dinshi Cesc Fabregas.

Fabregas mai shekaru 23, a baya sau biyu Arsenal taki amince da tayin Barcelona akanshi.

Gazidis ya shaidawa BBC cewar "babu hujjar tunanin a barshi ya tafi".

"kasuwancin na tafiya kalau, hakan na bamu karfi idan muka bayyana cewar ba zamu sayarda da Cesc Fabregas don mu samu kudi,"in ji Gazidis.

Ya kara da cewar "Cesc nada yarjejeniya mai tsawo damu".

Fabregas wanda ya taimakawa Arsenal ta doke Barcelona daci biyu da daya a bugun farko na gasar cin kofin zakarun Turai, ya bar kulob din Catalan ne a shekara ta 2003 a matsayin dan shekaru 16.