'Yan jarida zasu sawa Rooney ido-Ferguson

ferguson
Image caption Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce 'yan jarida zasu sawa Wayne Rooney ido, bayan da ya tsallake rijaya da baya a wasan da United ta lallasa Wigan daci hudu da nema.

Kocin Wigan Roberto Martinez yace kamata yayi abaiwa Rooney jan kati bayan ya yiwa James McCarthy gula da hannu.

Martinez yace"ga abin kuru-kuru, ya doke shi a fuska".

Amma Ferguson yace"babu komai, amma nasan 'yan jarida ne zasu nemi sai an hukunta Wayne".

Magoya bayan Wigan sun nuna bacin rai bayanda alkalin wasa ya baiwa Rooney katin gargadi bayan da McCarthy ya fadi sakamakon bugun da Rooney ya mashi.

Bayan mintun tara United ta samu nasara ta hannun Javier Hernandez.