Qatar ta nada Rajevac a matsayin Koci

rajevac
Image caption Milovan Rajevac

Qatar ta nada Milovan Rajevac a matsayin mai horrada 'yan kwallon kasarta.

A ranar daya ga watan Maris ne Rajevac dan kasar Serbia zai kama aiki har zuwa lokacin gasar cin kofin duniya a shekara ya 2014.

Rajevac wanda ya jagoranci Ghana zuwa gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010 ya maye gurbin Bruno Metsu wanda Qatar ta kori a watan daya gabata.

Kocin ya ce babban burinshi shine ya tsallakar da Qatar ta samu gurbi a gasar cin kofin duniya na Brazil a shekara ta 2014 da kuma na gasar cin kofin kasashen nahiyar Asiya a 2015.

Shugaban hukumar kwallon Qatar Sheik Hamad bin Khalifa Al Thani ya ce sun zabi Rajevac ne saboda kwarewarsu a harkar kwallon yankin.