West Ham ta kawo karshe haskakawar Liverpool

parker Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Scott Parker

West Ham United ta kawo karshen haskakawan da Liverpool ke yi karkashin jagorancin Kenny Dalglish inda Hammers din suka samu galaba daci uku da daya.

Wasannin takwas Liverpool ta buga ba tare da an doke ta ba, sai a ranar Lahadi West Hammer ta hannun Scott Parker da Demba Ba da kuma Carlton Cole ta samu nasara a yayinda Glen Johnson ya farkewa Liverpool kwallo daya.

Sakamakon wasannin gasar premier:

*Aston Villa 4 - 1 Blackburn Rovers *Everton 2 - 0 Sunderland *Newcastle United 1 - 1 Bolton Wanderers *Wigan Athletic 0 - 4 Manchester United *Wolverhampton … 4 - 0 Blackpool *Manchester City 1 - 1 Fulham