Arsenal ta tafka hasarar pan miliyan biyu da rabi

emirates
Image caption Filin Emirates na Arsenal

Kungiyar Arsenal dake taka leda a gasar premier ta tafka hasarar pan miliyan biyu da rabi cikin watanni shidan karshe na bara.

Hasarar da Arsenal tayi nada nasaba ga rashin sayarda 'yan kwallo.

A bara dai babu manyan 'yan wasan da Arsenal ta cefanar sabanin yadda lamarin yake a shekara ta 2009.

Gabda rufe kakar wasa ta 2009, Arsenal ta samu kusan pan miliyan arba'in wajen musayar 'yan kwallo hadda Kolo Toure da Emmanuel Adebayor wadanda ta siyarwa Manchester City.

Sai dai a kakar wasan data wuce kulob din ya samu pan miliyan hudu ne kacal wajen sayarda 'yan kwallo.

Arsenal a halin yanzu ta nanata aniyarta na cigaba da rike manyan 'yan wasanta kamarsu Cesc Fabregas bisa kalaman shugabanta Ivan Gazidis.

Bugu da kari izuwa 30 ga watan Nuwamban bara Arsenal ta buga wasanni 10 ne a filinta na Emirates sabanin wasanni 12 data buga a daidai wannan lokacin a shekara ta 2009.