Dan Najeriya Emenike ya soma murmurewa

emenike
Image caption Emmanuel Emenike

Dan kwallon Najeriya Emmanuel Emenike ya soma murmurewa a yayinda yake kokarin ganin ya warke don shiga fafatawar kasar da Ethiopia a wata mai zuwa, a wasan neman gurbi a gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da za ayi a shekara ta 2012.

Dan kwallon mai shekaru 23, a fidda shi tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a wasan daya bugawa Najeriya na farko tsakaninta da Saliyo a ranar tara ga watan Fabarairu.

Dan wasan Karab├╝kspor na Turkiya zai shafe makwanni shida baya taka leda saboda rauni a gwiwa.

Emenike ya shaidawa BBC cewar "abun baiyi dadi ba,amma ina samun sauki a kullum".

Kocin Super Eagles Samson Siasia wanda ya shawo kan Emenike ya bugawa Najeriya, ya ce yana fatar dan kwallon zai warware kafin wasansu na gaba.