Hukumar FA ba zata hukunta Rooney ba

rooney
Image caption Wayne Rooney

Hukumar dake kula da kwallon Ingila FA ba zata hukunta Wayne Rooney na Manchester United ba duk alamun ya yiwa dan wasan Wigan James McCarthy gula da hannu.

Lamarin ya auku ne a wasan gasar premier ta ranar Asabar a filin wasa na DW inda Rooney yaci kwallo daya cikin hudu da United ta doke Wigan.

Da aka sake duba bidiyon wasan a talabijin, anga Rooney ya yiwa McCarthy gula a kai.

Alkalin wasa Mark Clattenburg ya bada bugu a lokacin amma dai kocin Wigan Roberto Martinez ya ce kamata yayi a kori Rooney daga wasan.

Clattenburg ya shaidawa FA a ranar Litinin cewar yana ganin ya dauki hukuncin daya dace, abinda ke nufin cewar FA din ba zata iya kafa kwamitin da'a don labadtar da Rooney ba.