Juventus ta tafka hasarar Euro miliyan 40

del piero
Image caption Alexandro Del Piero na Juventus

Mahukunta Juventus sun sanarda cewa kungiyar ta tafka hasarar kusan Euro miliyan 40 a watanni shida na farko a kakar wasa ta 2010-11.

A dai dai irin wannan lokacin a kakar wasan data wuce, kulob din ya samu ribar Euro miliyan goma sha hudu.

Kudaden shiga da kulob din ya samu a watanni shida sune Euro Miliyan 88.8 wato faduwa kenan da kashi ashirin da tara cikin dari idan aka kwatanta da Euro miliyan 125 na bara.

Alkaluman sun alakanta faduwar da Juventus tayi saboda shiga gasar Europa wanda bai kai darajar gasar zakarun Turai ba, da kuma yadda aka rarraba kudaden harajin mallakar kallon gasar serie A tsakanin kulob kulob na Italiya.

Mahukunta kulob din sun kara da cewar suna saran karin faduwa daga yanzu har zuwa karshen kakar wasa ta bana.