Mourinho ya soki salon Deportivo

Jose Mourinho
Image caption Jose Mourinho yana gana wa da 'yan jaridu

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya soki salon wasan Deportivo La Coruna bayan da suka tashi canjaras a wasan da su ka buga a karshen makon da ya wuce.

Real Madrid ta mamaye zagaye na biyu na wasan, amma ba tare da ta samu damar zira kwallo ba, abinda ya sa ya soki salon La Coruna.

"Mun buga wasa ne da mai tsaron gida daya da kuma 'yan baya guda goma a zagaye na biyu. Kulob daya ne ya buga wasa domin neman nasara, yayin da dayan ya fito domin kare kansa".

Mourinho ya kuma soki wadanda ke tsara wasa a Spain, inda ya ce bai kamata a sa musu wasa ranar Asabar ba, bayan sun buga wasan zakarun Turai a tsakiyar mako.

"Wannan ba shi ne karo na farko ba, sun sha yi mana haka, sannan su koma gefe suna yi mana dariya," a cewar Mourinho.