Aston Villa ta tafka hasarar pan miliyan 37

houllier
Image caption Gerrard Houllier

Kungiyar Aston Villa ta ce zata rage yawan kudaden da take kashewa saboda tafka hasarar fiye da pan miliyan talatin da bakwai a karshen watan Mayun 2010.

Yawan albashin da kungiyar ke biya ya karu da kusan pan miliyan tara inda adadin ya zaman pan miliyan tamanin.

Aston Villa na samun pan miliyan hamsin da biyu daga haraji na kallo a gidajen talabijin a yayinda kudaden da suke samu daga shiga filin wasa ya tasamma pan miliyan 24.

To amma duk da hasarar da Villa tayi, ta shiga cikin sawun kungiyoyin kwallon kafa ashirin wadanda suka fi arziki.

Har wa yau Randy Lerner mai kungiyar Aston Villa ya baiwa kulob din pan miliyan ashirin da uku da rabi don siyo Darren Bent a watan Junairu.