2014:Watakila a ragewa Afrika yawan wakilai

fifa
Image caption Tsohon shugaban Brazil Da Silva

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa na tattaunawa akan yadda zata baiwa kowacce nahiya, yawan gurbin kasashen da zasu wakilceta a gasar cin kofin duniya a 2014.

Kasashe shida ne suka wakilci Afrika a gasar shekara ta 2010, saboda Afrika ta Kudu ce ta dauki bakuncin gasar.

Sai dai bisa dukkan alamu kasashe biyar ne zasu wakilci nahiyar saboda a Brazil za ayi gasar ta gaba.

Akwai yiwawar a rage yawan kasashen daga biyar ganin cewar wasu yankunan na matsin lamba akan cewar a kara musu gurbi.

Ghana ce kadai cikin sauran kasashe shidan Afrika, ta wuce zagayen farko a 2010, abinda kuma watakila zai iya shafar kasar.

A ranar Alhamis ne Fifa zata bada sanarwa akan hukuncin data yanke, bayan kamalla taron na kwanaki biyu a Zurich.