Bana matsawa Kaka ya murza leda kamar da

mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce baya yiwa dan kwallon Brazil Kaka matsin lamba don ya komo murza leda yadda ya saba,tun bayan daya murmure daga rauni.

Mourinho ya shaidawa manema labarai cewar"Kaka ya shafe watanni shida baya kwallo don haka sai a hankali zai gano bakin zaren kamar da".

Dan wasan mai shekaru 28, an yi mashi tiyata a gwiwa a ranar biyar ga watan Agusta amma sai a watan Disamba ya dawo taka leda.

Mourinho ya gayyaci 'yan kwallo ashirin cikin tawagarshi da zasu fafata da Malaga a ranar Alhamis a filin Bernabeu.

Sergio Canales da Pedro Leon na daga cikin 'yan kwallon da watalika zasu buga.

Amma dai Pepe da Ezequiel Garay da Sami Khedira da kuma Gonzalo Higuain basa cikin wadanda aka gayyata.