'Ya kamata Ferguson ya nemi ahuwa'- in ji Kungiyar kwagado

Kungiyar kwadago a Burtaniya ta ce bata yadda da furucin da kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya yi a kan alkalin wasan Martin Atkinson.

Kungiyar ta ce dolene Ferguson ya janye kalaman nasa kuma ya bada hakuri.

Ferguson dai zargi alkalin wasan Martin Atkinson da rashin adalci a wasan da Manchester to buga da Chelsea a filin Stamford Bridge in da ta sha kashi da ci biyu da daya.

"Kalamun Ferguson na da hatsari ga ayyukan alkalan wasa, domin haka dolene ya janye kalaman nasa kuma na nemi ahuwa". In ji Alan Leighton wani jami'i a kungiyar kwadago.

Dokokin hukumar FA ta Ingila dai ta haramta sukan alkaln wasan, kuma akwai yiwuwar Ferguson ya fuskanci fushin FIFA.