An kwantar da Guardiola a asibiti saboda ciwon baya

pep Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pep Guardiola

An kwantar da kocin Barcelona Pep Guardiola a asibiti saboda kashin bayansa ya goce.

Kulob din ya sanarda cewar mai horadda 'yan kwallonsa mai shekaru arba'in yana fama da matsanancin ciwon baya, a don haka ana yi mashi magani.

Gwaje gwajen da aka gudanar akan Guardiola ya nuna cewar akwai 'yan matsaloli a bayanshi wanda ke bukatar a tantance yadda za a magance.

Makwanni biyu kenan da Guardiola ke fama da ciwon baya, abinda kuma ya sanya shi kauracewa horon 'yan kwallonshi da aka yi a ranar Alhamis.

A ranar Laraba dai Barcelona ta doke Valencia daci daya me ban haushi inda Lionel Messi ya zira kwallon, kuma wannan ne karon farko da Barca ta samu galaba akan Valencia a gidan Valencia din, tun zuwanshi Nou Camp.

A makon daya gabata ne Guardiola ya sabunta yarjejeniyarshi na karin shekara guda don cigaba da jan ragama a Barcelona.