Platini ne yafi dacewa ya kalubalanci Blatter-Pele

pele
Image caption Pele na Brazil

Shahararren dan kwallon Brazil Pele ya ce shugaban hukumar kwallon Turai Uefa Michel Platini ne dai dai ya kalubalanci Sepp Blatter a takarar shugabancin Fifa.

Pele ya ce"Platini wanda a yanzu shine shugaban Uefa, yanada babbar dama na takara da Blatter".

Platini da Mohamed bin Hammam dan kasar Qatar wanda ke shugabantar hukumar kwallon nahiyar Asiya sune mutane biyu da ake gannin zasu kalubanci Blatter, wanda ke neman takarar shugabancin Fifa a karo na hudu.

Da Platini da Hammam har yanzu basu tabbatar da cewa zasu yi takara ba.

Shi dai Pele tun ba yanzu ba yace baida sha'awar shugabantar Fifa.

Shugabancin Blatter a Fifa dai ya fuskanci kakkausar suka sakamakon zaben Rasha da Qatar su dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.