Kocin Togo ya ajiye aikinsa

Kocin tawagar kwallon kafa ta Togo, Thierry Froger, ya ajiye aikinsa a yayin da ya koma kungiyar Nimes da ke Faransa.

Kocin ya bada takardar ajiye aikin nasa ne ga Hukumar kwallon kafan kasar, in ji mai magana da yawun kungiyar Komla Ekpe.

"Froger ya nemi hukumar da ta soke kwantaraginsa, saboda wasu dalilai na kansa, kuma bai bukaci a bashi wani kudi ba." In ji Ekpe.

Amma a ranar laraba Kungiyar Nimes da ke Faransa ta bayana Froger a matsayin kocin ta.