Ferguson zai kalubalanci tuhumar da ake yi masa

Image caption Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce zai kalubalanci tuhumar da Hukumar ta FA ta Ingila ke yi masa na laifin rashin da'a.

Kocin dai ya ce gwiwarsa ta yi sanyi ne a lokacin da aka bayyana sunnan Martin Atkinson a matsayin alkalin wasan da zai hura wasan da kungiyar za ta kara da Chelsea a filin Stamford Bridge.

United dai ta sha kashi ne a hannun Chelsea da ci biyu da nema a wasan.

A hirar da ya yi da gidan talbijina United bayan wasan, Ferguson ya kara da cewa alkalin wasan bai yi musu adalci ba.

Akwai yiwuwar Hukumar FA ta dakatar da kocin na tsawon wasanni biyu, indan ya gagara kare kansa daga tuhumar da ake yi masa.