An dakatar da Toure saboda haramtattun kwayoyi

Image caption Kolo Toure

Kungiyar Manchester City ta dakatar dan wasan bayan ta saboda an same shi da laifin shan haramtattun kwayoyi.

Hukumar FA ta Ingila ta sanarda da dan wasan mai shekarun haihuwa 29 cewa an same shi da laifin shan haramtattun kwayayi bayan gwaji da aka yi mishi a watan da ya gabata a wasan da City ta kara da United.

Hukunci wannan laifi dai sun hada da gargadi da kuma dakatarwa na tsawon shekara biyu.

A wata sanarwa da ta fitar City ta ce ta dakatarda dan wasan ne har sai hukumar FA ta kammala shari'a a kansa.