Za a kara ladabtarda Diouf da Bougherra na Rangers

diouf Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption El Hadji Diouf

Watakila 'yan kwallon Rangers Madjid Bougherra da El Hadji Diouf zasu kara fuskantar karin ladabtarwa sakamakon dabi'un da suka nuna a wasansu da Celtic na ranar Laraba.

Duka 'yan wasan biyu an dakatar dasu na wasa guda a gasar cin kofin kasar Scotland a Celtic Park.

Amma dai an saka batun rashin ladabinsu a rahoton Calum Murray.

Bougherra ya ruko hannun alkalin wasa Murray a lokacin daya nemi bashi jan kati a yayinda shi kuma Diouf ya wurgawa magoya bayan Rangers rigarshi bayan da aka kore shi.

An dai baiwa Diouf dan kasar Senegal jan kati ne bayan alkalin wasa ya hura tashi.

A halin da ake ciki a yanzu dakatarwar da aka yi musu zata yi aiki a wasansu na cin kofin Scotland a kakar wasa mai zuwa.