Mun sadaukar da nasararmu ga Toure-Mancini

kolo Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kolo Toure

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce sun sadaukar da nasararsu akan Wigan ga dan kwallonsu da aka dakatar Kolo Toure.

Toure na cikin 'yan kallo City ta samu galaba saboda dan kasar Ivory Coast din an dakatar dashi bisa zargin shan haramtattun kyayoyi masu kara kuzari.

Labarin zargin dan wasan mai shekaru 29 yana shan kwayoyi masu kara kuzari, ya fito ne kafin wasan City da Aston Villa a ranar Larabar data wuce na gasar cin kofin FA.

Mancini yace"Wannan nasarar ta Kolo ce, saboda yana cikin mawuyacin hali, amma dai muna sonshi".

Hukuncin da za a dauka akan Kolo ya soma ne daga gargadi zuwa dakatarwa ta shekaru biyu.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce abinda jinin Toure ya nuna kamar ya sha haramtattacen kwaya shine saboda yana shan kwayoyi rage kiba na matarshi.