2012:Najeriya za ta kara da Ethiopia a Abuja

nijeria
Image caption Super Eagles

Najeriya zata kara da Ethiopia a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika na 2012 a birnin Abuja a memakon Legas a ranar 26 ga watan Maris.

Hukumar kwallon Najeriya NFF ta ce wasan na rukunin B za a buga ne a babban birnin tarayyar kasar sabanin Legas inda a baya aka saran buga wasan.

'Yan wasan Super Eagles sun ce babban filin wasa na Teslim Balogun dake Legas baida dadin wasa saboda ciyawar roba.

Za a buga wasan ne da karfe tara na dare.

A watan daya gabata an yiwa 'yan wasan Najeriya ihu bayan da suka doke Saliyo da ci biyu da daya a wasan sada zamunci a birnin Legas.

A halin yanzu dai Guinea ce ke jan ragama a rukunin B a yayinda Najeriya ke ta biyu.