Bamu yanke kaunar lashe gasar premier ba-Cech

cech
Image caption Peter Cech

Golan Chelsea Peter Cech ya ce kulob din bai yanke kauna ba akan lashe gasar premier ta bana.

A halin yanzu United ta dara Chelsea da maki 12 amma kuma Blues din nada kwantan wasanni biyu, kuma zasu kara da United din a Old Trafford a watan Mayu.

Cech ya ce "Kunga cewar kulob kulob suna ta rasa maki,a don haka ina ganin cewar zamu iya kare kofinmu".

Chelsea ta casa United daci biyu da daya a ranar Talata data wuce, abinda kuma ke nuni cewar Chelsea ta farfado wajen ganin cewar ta kare kofin data lashe a kakar wasa ta bara.

Shi dai kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya gargadi 'yan wasanshi cewar kada su raina Blackpool saboda nasara zata taimakawa kungiyar a yinkurinta na sake lashe gasar premier.