Hukumar FA na goyon bayan kalubalantar Blatter

blater
Image caption Sepp Blatter da Muhammed Bin Hammam

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Ingila wato FA ta ce zata goyi bayan amintaccen mutumin da zai kalubalanci Sepp Blatter a takarar shugabancin Fifa.

Wata majiya ta ce hukumar FA din na duba yiwuwar rubuta wasika ga shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya Muhammed Bin Hammam na Qatar akan cewar ya fito takara zata goyi bayanshi.

Blatter mai shekaru 75 yana kokarin sake takara a karo na hudu ne a watan Yunin bana, amma dai Bin Hammam ya bayyana cewar ya kamata a samu sauyi, saboda a cewarshi dadewar Blatter na jawo zarge zarge akan Fifa.

Bisa dukkan alamu dai hukumar FA ta Ingila har yanzu tana cikin fushi bisa rashin samun damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya da za ayi a shekara ta 2018, abinda yasa wasu ke ganin sun sanwa Blatter kahon zuka.

Shi dai tsohon shahararren dan kwallon Brazil Pele, ya nuna cewar Michel Platini wato shugaban hukumar kwallon Turai ne yafi dacewa ya maye gurbin Blatter a watan Yuni.