Ferguson ya ki ganawa da manema labarai

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson, ya ki ganawa da manema labarai bayan da kungiyarsa ta sha kashi a hannun Liverpool da ci uku da guda a filin Anfield.

Kocin bai gana da tashar talabijin ta Sky Sports ba da kuma tashar radio ta TalkSports wanda aka daura alhakin yadda bayanai da hira kan wasan Premier, da kuma gidan talbijin ta Manchester, MUTV.

Mataimakin kocin Mike Phelan bai gana da BBC ba bayan wasan kamar yadda ya saba.

Kungiyar ta dau matakin tun kafin Manchester ta fara wasan.

Idan har kafofin yadda labaran su ka kai kara Hukumar Premier, Hukumar za ta daukin mataki a kan kocin.