Steve Kean na nan daram a Blackburn-Venky's

kean Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Steve Kean

Kamfanin dake da kungiyar Blackburn Rovers wato Venky's ya karyata cewar aikin kocin kulob din Steve Kean na cikin barazana sakamakon samun maki guda cikin wasanni biyar na gasar premier.

Rovers ta dara rukunin kulob din da zasu nitse da maki biyu, a yayinda rahotanni ke cewar Kean wanda ya maye gurbin Sam Allardyce a watan Disamba yana fuskantar matsin lamba.

Kakakin kamfanin Venky's Anuradha Desai ta ce babu gaskiya a rahoton.

Tace" babu batun sauya koci, zai cigaba da rike mukaminshi".

Kean mai shekaru 43, ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da rabi tare da Blackburn a watan Junairu.