Van Gaal zai bar Bayern Munich a watan Mayu

van gaal
Image caption Louis Van Gaal

Kungiyar Bayern Munich ta sanarda cewar mai horadda 'yan kwallonta Louis van Gaal zai barta a karshen kakar wasa ta bana.

Hakan na nufin cewar zai tafi shekara guda kafin kwangilarshi ta kare, bayan da aka doke Bayern a wasanni uku a jere na gasar Bundesliga sannan tana tangal tangal a gasar zakarun Turai.

A cewar sanarwar da kungiyar ta fitar"hujjar katse kwangilar itace sabanin dabarun da ya kamata ayi amfani dashi a kulob din".

A halin yanzu zakaran kwallon Jamus din ce ta biyar akan tebur na gasar Bundesliga sannan ta gaza da maki bakwai wajen neman gurbin zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasannin mai zuwa.

Shugaban Bayern Karl-Heinz Rummenigge ya ce "idan aka duba yanayin da muke ciki a yanzu, da kamar wuya mu tsallake zuwa gasar zakarun Turai".

Van Gaal ya koma Bayern Munich ne a shekara ta 2009 bayan ta kori Jurgen Klinsmann saboda kasa taka rawar gani.