2012:Kamaru zata kafa sansani a Portugal

lions
Image caption Indomitable Lions

Kamaru za ta kafa sansanin horo a Portugal a shirye shiryenta na fuskantar Senegal a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika na 2012.

Za a buga wasan na rukunin E tsakanin Indomitable da Teranga Lions a ranar 26 ga watan Maris a Dakar.

Zakarun kwallon Afrika har sau hudu zasu yi horon a Lisbon amma ba a sanya rana ba.

Kocin Kamaru Javier Clemente ya ce an zabi Portugal ne a matsayin wajen horon saboda nan ne yafi dace wa a shiryawa fafatawar.

A halin yanzu dai Teranga Lions ce ke jan ragama a rukunin E da maki shida bayan ta doke Congo da Mauritius.

A yayinda ita kuma Kamaru keda maki hudu, amma Clemente ya ce zasu takawa Senegal birki.

A daya wasan rukunin E din dai Congo zata dauki bakuncin Mauritius a Kinshasa.