Higuain zai koma taka leda a watan Aprilu

higuain
Image caption Gonzalo Higuain ya kwantar da Puyol

Dan wasan Real Madrid Gonzalo Higuain ya samu sauki matuka daga tiyatar da aka yi mashi,kuma watakila ya buga wasansu da Barcelona a wata mai zuwa na cin kofin Kings.

Dan kwallon Argentina din an yi mashi tiyata a wani asibiti a Chicago saboda gocewar kashi.

Kocin Real Jose Mourinho ya nuna jin dadi game yadda yaga Higuain ke murmurewa, kuma yana saran zai buga wasansu na ranar 20 ga watan Aprilu a filin wasa na Bernabeu tsakaninsu da Barcelona.

Akwai alamun cewar zai iya buga wasan zagayen gabda na kusada karshe na gasar zakarun Turai, idan har Real ta fidda Lyon.

Higuain dai ya fara horo a makon daya gabata a karon farko tunda aka yi mashi tiyata.

Dan kwallon mai shekaru 23, asali yana fara wasan Real ne tare da Christiano Ronaldo.

Real ta siyo dan kwallon Togo Emmanuel Adebayor daga Manchester City a watan Junairu don maye gurbin Higuan kafin ya murmure.

Higuain ya koma Real Madrid ne a watan Junairu a 2007daga kungiyar River Plate ta Argentina.