Gerrard ba zai buga wasan Liverpool da Braga ba

gerrard
Image caption Steven Gerrard

Kaptin din Liverpool Steven Gerrard ba zai buga wasansu da Barga ba a Portugal na zagaye na biyu na gasar Europa.

Liverpool ce ta sanarda ta hakan, amma bata bada hujjar cire dan kwallon a wasansu na ranar Alhamis din ba.

A baya bayan nan Gerrard yayi fama da rauni, amma kuma ya buga minti casa'in na wasan da suka doke United da ci uku da daya a ranar Lahadi.

Amma ana saran sabon dan wasa Andy Caroll zai buga wasan.

Shugaban likitocin Liverpool Peter Brukner ya ce duk da cewar Fernando Torres ya bar Liverpool ya koma Chelsea, amma dai kulob din na kan hanya tunda shima Caroll ba kanya lasa bane.