Hargreaves zai bar United a karshen kakar wasa ta bana

hargreave
Image caption Owen Hargreaves

Akwai alamun Owen Hargreaves zai bar Manchester United a karshen kakar wasa ta bana saboda kulob din yaki amince ya sabunta kwangilarshi.

Dan kwallon mai shekaru talatin yayi ta fama da rauni mai tsanani tun bayan da yazo United daga Bayern Munich a shekara ta 2007 akan pan miliyan 18.

A watan daya wuce Sir Alex Ferguson bai saka Hargreaves cikin jerin tawagar 'yan kwallonshi 25 da zasu buga gasar cin kofin zakarun Turai.

A halin yanzu dai dan wasan yana jinyar rauni kuma babu tabbacin ranar da zai komo taka leda.

Wasa na minti shida kacal Hergreaves ya buga tun watan Satumban 2008, a yayinda aka yi mashi tiyata a gwiwowinshi biyu abinda ke barazana ga rayuwarshi ta kwallo.