Kocin Saliyo Lars Olof Mattsson zai cigaba

olof
Image caption Lars Olof Mattsson

Lars Olof Mattsson na bukatar ya cigaba da kasancewa kocin Sierra Leone har zuwa karshen wasannin share fage na neman gurbi a gasar cin kofin duniya a 2012.

Kocin dan kasar Sweden, ya kamata kwangilarshi ta kare a ranar 27 ga watan Maris bayan wasansu da Nijer.

Wani kamfanin simintia a kasar ya amince ya biya Mattsson dala dubu goma na karin wa'adin.

Amma dai dan shekaru hamsin da shidan ya shaidawa BBC zai zauna har sai bayan wasan karshe na share fagen.

Mattsson ya ce "ina murnar wannan damar, tare da fatar za a kara bani wata damar".