UEFA na tuhumar Wenger da Nasri

wenger Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Arsene Wenger da Massimo Busacca

Hukumar dake kula da gasar kwallon kafa a Turai Uefa na tuhumar kocin Arsenal Arsene Wenger da Samir Nasri akan kalaman da suka yiwa alkalin wasa bayan Barcelona ta fiddasu a ranar Talata.

Wenger yayi musayar kalamai da alkalin wasa Massimo Busacca bayan kashin da gunners ta sha daci uku da daya a gasar zakarun Turai.

Wenger ya nuna rashin jin dadi akan hukunci korar Robin van Persie a lokacin wasa na daya da daya a minti na hamsin da shida.

Uefa tayi nazari akan rahoton Busacca kafin ta tuhumi Wenger da Nasri.

A ranar 17 ga watan Maris, kwamitin da'ar Uefa zata saurari karar.