Wenger ya yi kuka da alkalin wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce sallaman da alkalin wasa ya yiwa Robin van Persie ne yasa Barcelona ta doke kungiyar shi da ci 3-1 a gasar zakarun Turai.

Van Persie dai ya samu katin gargadi na biyu ne a lokacin daya durma kwallo, bayan da alkalin wasa ya hura husir.

Van Persie dai ya je bai ji lokacin da alkalin wasan ya hura husir din ba, saboda ihun da dimbin mutane ke yi a filin wasan.

Wenger ya ce: "Na yi magana da jami'an Uefa, kuma suma sun kadu da hukuncin da alkalin wasan ya dauka a wannan irin wasa mai mahimmanci.

"Me yasa za'a sallame shi? da ya tade wani ne, bamu komai, amma gaskiya alkalin ya bamu kunya." In ji Wenger.