Fabregas ba zai buga wasansu da United ba

fabregas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cesc Fabregas

Kaptin din Arsenal Cesc Fabregas ba zai buga wasansu na cin kofin FA da Manchester United ba a ranar Asabar, amma Robin van Persie zai buga.

Kocinsa Arsene Wenger ya ce Fabregas na fama da rauni a kafadarshi kuma watakila ya shafe makwanni yana jinya.

Gola Wojciech Szczesny shima ba zai buga a wasan zagayen gabda na kusada karshe a Old Trafford ba saboda raunin da yaji a wasansu da Barcelona.

Gannin cewar yanzu dai gola daya me lafiya ne ya ragewa Wenger, watakila ya bukaci golan aro.

A cewar Wenger, Szczesny zai yi jinya na wani dan lokaci, sannan Lukasz Fabianski shima zai dade yana jinya.