Siasia ya gayyaci 'yan kwallo 24 don fuskantar Ethiopia

siasia
Image caption Samson Siasia

Kocin Super Eagles na Najeriya Samson Siasia ya gayyaci 'yan kwallo ashirin da hudu don fuskantar Ethiopia a wasan share fage na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012.

A karon farko tun bayan kamalla gasar cin kofin duniya, an gayyaci Martins Obafemi cikin tawagar Super Eagles, sannan an gayyaci sabon dan kwallon baya Efe Ambrose da kuma Victor Anichebe na Everton.

Shima Ike Uche wanda ya shafe kusan shekara guda yana jinya, ya samu shiga cikin wadanda aka gayyata.

A ranar 14 ga wannan watan 'yan kwallon dake taka leda a Najeriya zasu shiga sansanin horo sannan bayan kwanaki biyar suma wadanda ke bugawa a kasashen waje ake saran zasu iso Abuja.

A ranar Lahadi 27 ga wannan watan ne za a buga wasa tsakanin Najeriya da Ethiopia da misalin karfe bakwai agogon kasar a babban filin wasa na Abuja.

A halin yanzu Najeriya ce ta biyu a rukuni na hudu da maki uku, a yayinda Guinea ke jan ragama da maki shida.

Masu tsaron gida:

1. Vincent Enyeama 2. Dele Aiyenugba 3. Chibuzir Okonkwo

'Yan wasan baya:

4. Olubayo Adefemi 5. Taye Taiwo 6. Elderson Echiejile 7. Joseph Yobo 8. Dele Adeleye 9. Efe Ambrose

'Yan tsakiya:

10. Mikel Obi 11. Obiora Nwankwo 12. Joel Obi 13. Fegor Ogude 14. Nnamdi Oduamadi 15. Kalu Uche 16. Ikechukwu Uche 17. Solomon Okoronkwo

'Yan gaba:

18. Ahmed Musa 19. Osaze Odemwingie 20. Victor Anichebe 21. Peter Utaka 22. Obinna Nsofor 23. Ekigho Ehiosun 24.Obafemi Martins