Dan Arsenal Djourou ba zai yi jinya har kakar wasa ta bana

djouro
Image caption Johan Djourou

Dan kwallon Arsenal Johan Djourou ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda targade a kafadarshi.

Dan shekaru ashirin da hudu da haihuwa,Djourou ya jimu ne a wasan da United ta lallasa Arsenal a gasar cin FA a filin Old Trafford.

Ya jimu ne bayan ya hadu da Bacary Sagna abinda yasa aka fidda shi a wasan.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce "abin takaici Johan Djourou ba zai kara taka leda har karshen kakar wasa ta bana".

Ya buga Gunners wasanni 29 a gasa daban daban a kakar wasa ta bana.