Ferdinand ba zai buga wasan Ingila da Wales ba

rio da capello
Image caption Rio Ferdinand da Fabio Capello

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce baya tunanin Rio Ferdinand zai murmure har ya bugawa Ingila wasanta da Wales a wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Turai a ranar 26 ga watan Maris.

Dan wasan mai shekaru 32 yana jinyar rauni a kafarshi tun a watan Fabarairu lokacin da United ta sha kashi a wajen Wolves.

Ferguson yace"Rio yana samun sauki,amma bai zai komo taka leda ba sai bayan wasan Ingila".

Rashin damar kaptin din Ingila Ferdinand ya buga wasan da Wales zai kara bude mahawara akan wanda za a baiwa kambum kaptin.

Tuni dai mataimakin kaptin Steven Gerrard aka gano ba zai buga ba saboda tiyatar da aka yi mishi.

A wasan Ingila da Denmark na sada zumunci, saboda Ferdinand da Gerrard basu buga ba, Frank Lampard ne ya rataya kaptin.