Kofin FA:Zamu doke Manchester United-Mancini

mancini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce 'yan kwallonshi zasu doke abokan hammayarsu Manchester United a wasan zagayen kusada karshe na gasar cin kofin FA da zasu buga a filin Wembley.

City zata kara da United a karshen makon 16/17 na watan Afrilu, bayan da Eastlands ta doke Reading daci daya me ban haushi a zagayen gabda na kusada karshe.

Mancini yace:"Mun kara sau biyu da Manchester United a kakar wasa ta bana, kuma mun taka rawar gani, a don haka muna damar tsallakewa zuwa wasan karshe".

Cikin kungiyoyin Manchester biyu duk wacce ta samu galaba zata hadu da Stoke ko Bolton a wasan karshe.

Mancini, wanda kungiyarshi ta sha kashi a wajen United daci biyu da daya a Old Trafford a watan Fabarairu, sun buga canjaras a watan Nuwamba a Eastlands.