Ya kamata Ghana ta lashe kofi a badi-Muntari

muntari
Image caption Sulley Muntari

Dan Ghana wanda ke taka leda a Sunderland Sulley Muntari ya ce lokaci yayi da Black Stars zata lashe wata gasa a duniya.

Ghana ta samu kyautar azurfa a gasar cin kofin Afrika na 2010 amma Muntari na ganin cewar a badi ya kamata su lashe gasar.

Yace"bamu da wata zabi, illa mu lashe gasa a badi wato gasar kwallon Afrika.

Dan kwallon mai shekaru 26 ba a gayyace shi cikin tawagar Black Stars a lokacin gasar kwallon Afrika a bara saboda dalilai na rashin da'a, amma kuma sai aka gayyaceshi zuwa gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Ghana zata kara da Congo a ranar 27 ga watan Maris a wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar kwallon kasashen Afrika na 2012.