Kamaru ta gayyaci Kameni don karawa da Senegal

kameni Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Carlos Kameni

Kocin Kamaru Javier Clemente ya maidoda golan kasar Carlos Kameni cikin tawagar 'yan kwallonshi da zasu fafata da Senegal a wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar Afrika a badi.

Amma ba a gayaci dan Arsenal Alex Song da kuma Achille Emana na Real Betis.

Dukka wadannan 'yan kwallon uku basu bugawa Indomitable Lions kwallo ba tun bayan gasar cin kofin duniya na bara.

Dan wasan Tottenham Hotspur Benoit Assou-Ekotto shima ba a gayyaceshi ba, amma Clemente ya kira 'yan kwallo uku dake taka leda a cikin kasar.

Abouna Ndzana da Julien Momasso da Andre Ndam Ndam na cikin tawagar a yayinda dan wasan Inter Milan Samuel Eto'o zai rataya kaptin.

A halin yanzu Kamaru ce ta biyu a rukunin E da maki hudu bayan wasanni biyu, sannan tana bayan Senegal da maki biyu.

Gololi: Guy Roland Ndy Assembe (Nantes, France), Idriss Carlos Kameni (Espanyol, Spain), Charles Itandje (Atromitos, Greece)

'Yan baya: Sebastien Basson (Tottenham Hotspur, England), Gaëtan Bong (Valenciennes, France), Benoit Angbwa (Anzhi Makhachkala, Russia), Jean-Patrick Ndzana Abouna (Astres Douala), Nicolas Nkoulou (Monaco, France), Henri Bedimo (Lens, France), Stephane Mbia (Marseille, France)

'Yan tsakiya: Matthew Mbuta Andongcho (Crystal Palace Baltimore, USA), Enoh Eyong Takang (Ajax Amsterdam, Netherlands), Landry Nguemo (Nancy, France), André Ndam Ndam (Coton Sport), Julien Momasso (Astres Douala), Aurélien Chedjou (Lille, France), Georges Mandjeck (Rennes, France), Benjamin Moukandjo (Monaco, France)

'Yan kwallon gaba: Eric-Maxim Choupo Moting (Hamburg, Germany), Somen Tchoyi (West Bromwich Albion, England), Achille Webo (Mallorca, Spain), Samuel Eto'o (Inter Milan, Italy), Vincent Abubakar (Valenciennes, France)