Arsenal na gabda dawowa da Jens Lehman

lehmann Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jens Lehmann

Arsenal na gabda kulla yarjejeniya da tsohon golanta Jens Lehmann don kasancewa da ita zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Sakamakon raunin da Wojciech Szczesny da Lukasz Fabianski da kuma Vito Mannone, a halin yanzu Arsenal nada Manuel Almunia a matsayin lafiyayyen gola daya tal.

Tsohon golan Jamus mai shekaru 41 ya bugawa Arsenal a wasanni 199 daga shekara ta 2003 zuwa 2008 kafin yayi ritaya a bara, bayan shafe shekaru biyu a Stuttgart.

Idan har aka kulla yarjejeniyar akan lokaci, za a iya saka Lehman cikin tawagar Arsenal don fafatawa da West Brom.

Arsenal a halin yanzu na bayan Manchester United da maki uku, kuma tana kokarin lashe kofi na farko tun shekara ta 2005.

Amma a makwanni biyun da suka wuce,an fidda Arsenal cikin gasa uku wato na kofin Carling dana FA da kuma na zakarun Turai.

Kafin zuwa Lehman Arsenal, ya taba kamawa a Schalke da AC Milan da kuma Borussia Dortmund.