Gallas zai yi jinyar kafada na wata guda

gallas
Image caption William Gallas

Dan kwallon Tottenham William Gallas zai shafe akalla wata guda yana jinya, bayan ya raunata kafadarshi.

Kocin Spurs Harry Redknapp ya bayyana cewar Gallas, wanda a kakar wasa ta bana yana kan ganiyarshi, ya fadi ne lokaci horo a ranar Talata.

Redknapp yace"labarin babu dadi saboda Gallas ya fadi, amma idan har jinyar mai tsawo ce tabbas zamu ji a jikinmu".

Gallas ya kasance kashin bayan Tottenham a gasar zakarun Turai na bana, inda ta tsallake zuwa zagayen gabda na kusada, musamman yadda suka fidda Inter Milan a zagaye na biyu.

Wani batu dake damun Redknapp a halin yanzu shine na raunin Wilson Palacios wanda zai yi jinya ta makwanni uku zuwa hudu.