Schalke 04 ta sallami kocin 'yan kwallonta Magath

magath
Image caption Felix Magath

Kungiyar Schalke 04 ta Jamus ta sallami mai horadda 'yan kwallonta Felix Magath ba tare da wata-wata ba.

Magath mai shekaru hamsin da bakwai ya lashe gasar Bundesliga tare da Wolfsburg da kuma Bayern Munich.

Sai dai a halin yanzu Schalke 04 ce ta goma akan teburin gasar kwallon Jamus din.

Koda yake dai Schalke ta tsallake zuwa zagayen gabda na kusada karshe a gasar zakarun Turai, bayan ta samu galaba akan Valencia daci uku da daya,amma bisa dukkan alamu hakan bai gamsarda mahukunta kulob din ba.

Shugaban Schalke Clemens Toennies ya ce "muna bukatar daukar matakan gaggawa don kwato kulob din".